Babbar jam’iyyar hamayya a Tunisia wacce ba ruwanta da hada harkar mulki da addini, tana ikirarin samun nasara a zaben kasar wanda zai shiga tarihi, domin shiga sabuwar majalisar dokokin kasar mai kujeru 217.
Jam’iyyar da ake kira Nidaa Tounes, tace kwarya-kwaryar sakamakon zabe ya nuna ta sami kusan kujeru 80, fiyeda kowace jam’iyya.
Jiya litinin jam’iyyar Ennahda mai mulkin kasar ta amince ta sha kaye, tana cewa zata amince da sakamkon zaben. Tsohon Firayim Ministan kasar Ali Larayedh, yayi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar su maida hankali kan zaben kasar na gaba.
Jam’iyyar Ennahda mai sassaucin ra’ayi addinin ta sami kusan kujeru 70.A hukumance dai har yanzu ba a bayyana sakamkon zaben ba.
Kimanin jam’iyu 90 ne suka shiga zaben da aka gudanar ranar lahadi, a matakin bin tafarkin demokuradiyya na baya bayan da kasar take dauka tun bayan da aka hambare gwamnati Ben Ali a 2011, al’amarin da ya janyo tashin-tashina a kasashen larabawa.