Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Afirka ta Kudu Ya Umarci 'Yansandan Kasar su Zakulo Wadanda Suka Kashe Meyiwa


Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu
Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu

Kwanan nan wasu suka kashe Meyiwa keftein kungiyar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu a gidan budurwarsa yayin da suke yunkurin yin sata

Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma yayi kira ga ‘Yansandan kasar suyi bakin kokarinsu su gano mutanen da suka kasashe keftin na kungiyar kwallon kafar kasar, su kuma gurfanar da su a gaban shari’a.

A daren Lahadi ne aka kashe Meyiwa dan shekaru 27 da haifuwa a gidan budurwarsa wata mawakiya a wani yunkurin sata.

A jiya Litinin ne Mr. Zuma ya fidda sanarwa yana mai cewa babu kalamai da zasu bayyana irin takaicin da ‘yan kasar suke ji kan wannan rashin.

Rundunar ‘Yansandan kasar tayi tayin zata bada tukuicin dala dubu 23 ga duk wanda zai bada bayanai da zasu kai ga kama wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Ahalinda ake ciki kuma, masu gabatar da kara a Afirka ta kudu sun ce zasu daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yankewa gurgun nan mai gudun yada kanin wani Oscar Pistorious a shair’ar kashe budurwarsa, da daurin shekaru biyar da kotu ta yanke masa.

A jiya Litinin ce kakakin hukumar lauyoyin gwamnatin kasar ta bada sanarwar haka.

XS
SM
MD
LG