Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Ragargaza Sansanoni Da Makwantan Boko Haram


Hukumomi suka ce da wannan wurin sansanin 'yan Boko Haram ne, amma sun gudu bayan da sojoji suka tinkare shi suka kwace
Hukumomi suka ce da wannan wurin sansanin 'yan Boko Haram ne, amma sun gudu bayan da sojoji suka tinkare shi suka kwace

Masu sukar lamiri sun ce ba matakin sojan da zai iya warware abubuwan da suka haddasa matsalar, yayin da hukumomi suka kama surakanan Abubakar Shekau suka tsare su.

Rundunar sojojin Najeriya ta fada litinin cewa farmakin da ta kaddamar watanni biyu da suka shige a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya cimma gurorinta da dama na ragargaza sansanonin 'yan bindiga, tare da kashewa ko kama mayaka da kuma kwato mutanen da aka sace aka yi garkuwa da su.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Birgediya-janar Chris Olukolade, yace an kuma saki wasu mata 23 da yara 35 wadanda aka tsare su bisa tuhumar su na tallafawa 'yan kungiyar Boko Haram, a wani matakin neman lallashin masu sassaucin ra'ayi cikin magoya bayan kungiyar.

Sojojin Najeriya sun kaddamar da yunkurinsu mafi girma ya zuwa yanzu na kawo karshen wannan tawayen shekaru 4 wanda ya kashe dubban mutane, ya kuma gurgunta al'amuran yau da kullum a sassa masu yawa na arewacin wannan kasa da ita ce lambawan cikin masu sayarda man fetur ga kasashen waje a Afirka.

Birgediya-Janar Olukolade ya ce, "aikin da aka ba sojojin shiu ne na ragargaza dukkan sansanonin 'yan ta'adda da kama wadanda suke aikatawa. An cimma akasarin wannan a bayan da aka ragargaza makwantan 'yan ta'adda. An kama 'yan ta'adda da yawa, wasu da dama sun mutu a bakin daga."

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ayyana dokar-ta-baci ranar 14 ga watan Mayu, ya umurci karin sojoji da su shiga yankin arewa maso gabas, a bayan da aka samu rahotannin cewa Boko haram ta kame kananan hukumomi da yawa a wannan yanki mai ciyayi da hamada.

Tun lokacin dai, majiyoyin tsaro sun ce yawan hare-haren da 'yan Boko Haram ke kaiwa ya ragu sosai, koda yake mummunan harin da aka kai kwanakin baya kan wata makaranta ya nuna cewa har yanzu kungiyar tana iya haddasa ta'asa.

Olukolade yace ragargaza sansanonin da suka yi ta sa wasu 'yan bindigar sun sulale sun koma cikin manyan garuruwa na yankin, kamar Maiduguri, inda aka kama da yawa daga cikinsiu a sumame da tarewa da binciken da ake gudanarwa.

A ranar lahadi ma dai, dakarun Najeriya sun ce sun gano wasu ramukan karkashin kasa masu yawa da aka gina, wadanda suka hada gidaje da kuma wasu ramukan buya na karkashin kasa a unguwar Bulabulin dake Maiduguri. Haka kuma, an gano kaburburan mutanen da aka ce 'yan kungiyar suka kashe.

Olukolade yace wasu daga cikin dakunan buya na karkashin kasa da aka gano, zasu iya daukar mutane 100.

Sai dai masu sukar lamirin wannan sun ce babu wani matakin sojan da zai iya warware batutuwan da suke kara iza wutar wannan matsala ta Boko Haram, watau bakin talaucin da arewacin Najeriya ke fama da shi, da kuma mayarda yankin saniyar ware a siyasance. Sai dai kuma kokarin neman tattauna sulhu da kungiyar ya ci tura.

Hukumomi sun kuma kama, suka tsare iyayen matar Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG