Rahotanni sun ce tun daga misalin karfe biyun daren jiya sojoji da 'yan sanda suka yi wa gidan kawanya bisa ga rahotannin siri da suka samu. Sun kwashe sao'i bakwai suna harbe kafin su samu su kashe daya daga cikin mutanen dake cikin gidan. Sun kama mutum daya da makamai da bama-bamai da dama. Sun kubutar da mata da yara kanana.
Yayin da yake jawabi Birigediya Tasiu Ibrahim ya ce sun kai samamen sabili da rahoton da suka samu cewa wasu 'yan ta'ada na cikin gidan. Ya ce sun sami nasarar samamen kwarai da gaske. Ya kuma nuna wa 'yan jarida kayan da suka samu a cikin gidan.
Makwafcin gidan ya ce kamar kwanaki shida ke nan da wadannan mutanen suka taso daga wani gida can nesa suka karbi gidan haya. Ya ce ya ji harbe-harbe lamarin da ya hanasu barci har gari ya waye. Ya ce jami'an tsaro sun yi masa tambayoyi kafin su sallameshi.
Murtala Faruk Sanyinna na da rahoto.