A cikin hirar da yayi da Muryar Amurka, Barrister Turaki yace wadanda suke taimakawa kwamitinsa domin ganin an samu sulhu a arewacin Najeriya, daga cikin jama'a har zuwa 'ya'yan kungiyar da suke tattaunawa da su, mutane ne da suke yin haka tsakani da Allah a saboda damuwar da suke da ita game da ganin an maido da zaman lafiya a wannan yanki.
Yace a duk tattaunawar da suke yi da 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram, babu wani bangaren da ya taba tayaer da wannan batu na tukuicin da gwamnatin Amurka ta ce zata bayar din.
Barrister Turaki yace 'yan kwamitinsa ba su ga yadda wannan abu zai kawo cikas ga ayyukansu ba, kuma da yardar Allah zasu cimma nasarar wannan yunkuri na samar da zaman lafiya mai dorewa a arewacin Najeriya.
Ga cikakken bayanin shugaban kwamitin...