Gwamnati ta yi la'akari da cewa tashe tashen hankula sun sa yunwa da fatara suna addabar mutanen yankin. Karamin ministan kudi Dr. Yarima Ngama ya ce shugaban kasa ya sauraresu ya bada kudi a sayi wadannan kaya a kaisu jihohi ukun.Misali shugaban ya bada buhun abinci dubu dari uku da casa'in. Kawo yanzu ana bukatar tireloli dari shida da hamsin na daukan abincin da kuma tireloli dari biyar na daukan masara ban da dawa da gyero. Ministan ya kara da cewa sanin kowa ne cewa jihar Borno ita ce tafi yawan jama'a cikin jihohin uku. Ita ce kuma tafi shiga cikin halin kakanikayi da rigingimu.Ta dalilin haka rabin abincin jihar Borno za'a kai. Kashi talatin da hudu za'a kai jihar Yobe. Adamawa zata samu kashi goma sha shida. Har wayau shugaban ya bada nera miliyan dari biyu da hamsin na sayen shinkafa da zannuwa da shadda da kayan masarufi.
Ga karin bayani daga Umar Fark Musa.