Tun ba'a yi nisa ba sai ga shi Shekau ya sake fitowa da sako inda ya musanta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnati. Maimakon hakan ya amince da kashe yaran makaranta da aka yi a Mamudo jihar Yobe ya kuma kara da barazanar dada kai hare-hare. To sai dai a wannan lokacin akwai ban-banci domin Marwana bai yi shiru kamar da can. Shi ma ya mayarda martani. Ya yi watsi da furucin Shekau ya kalubale shi ya fito ya yi hare-haren. Ya sake jaddada abubuwan da ya fada makon jiya cewa suna neman zaman lafiya. Sun yafe duk abun da aka yi masu. Su ma suna neman gafara daga al'umma duka. Ya ce a wannan watan azumi mai alfarma suna fatan kowa ya zauna lafiya a cigaba da addu'a.Ya ce yana tabbatarwa kwamitin da gwamnati ta kafa da gwamnati kanta da Musulman Najeriya su ji abun da shi Marwana ya fada su yi watsi da furucin Shekau. Ya ce a wannan karon kowanene ya ja baya zasu barshi a baya, wato kamar yana yiwa Shekau hannunka mai sanda ne.Ya ce idan gwagwarmaya Shekau zai yi shi kadai zai yi. Marwana ya ce shi ya cewa mujahidansu su bari kuma ba za'a yi ba. Ya ce shi Shekau ya fito ya ce a yi din mutane su gani. Ya kira mutane su daina saurarensa ko jin tsoron furucinsa.
Daga karshe ya tabbatar cewa nan ba dadewa ba za'a tara mujahidan bisa ga shirin zaman lafiya. Ya tabbatarwa kwamitin neman sulhu ba za'a ji kunya ba sai shi Shekau mai neman tada hankali.
Ga rahoton Abdulwahab Mohammed.