A cikin wannan watan ne madugun kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fada a cikin wani faifan bidiyo cewa kungiyar ta sace wasu mata da yara da yawa domin mayarda martani ga jami'an tsaron da yace su na kama mata da 'ya'yan membobin kungiyar ba tare da dalili ba.
A farmaki mafi girma da ta kaddamar tun lokacin da 'yan Boko Haram suka fara tayar da kayar baya a shekarar 2009, rundunar sojojin Najeriya tana kokarin fatattakar masu kishin addinin daga yankunan da suka kakkafa cibiya a dab da tabkin Chadi a bakin iyakar Najeriya da Kamaru, Chadi da Nijar.
Wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka, Nasiru Adamu el-Hikaya, ya aiko da rahoto daga Abuja kan taron da kakakin rundunar sojoji, Birgediya-janar Chris Olukolade, ya kira dangane da kwato mata da yaran.