Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Ina Boko Haram Take Samun Kudaden Gudanar Da Ayyukanta?


Imam Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko-Haram.
Imam Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko-Haram.

Da alamun kungiyar tana da hanyoyin samun kudade masu yawa, amma masana sun ce saninsu na da wuya.

A duk lokacin da rundunar sojan Najeriya ta bayyana samun wata nasara a kan ‘yan Boko Haram, tana hadawa da lissafin irin makaman da ta kama. A can baya dai, akasarin makaman bindigogi ne kirar AK-47, da harsasai da kuma bama-bamai.

Amma a cikin ‘yan kwanakin nan, makaman sun fara hadawa da bindigogin da aka girka kan motoci, da na kabo jiragen sama da na harbin tankokin yaki.

Mai fashin bakin siyasa, Nwachukwu Oriji, yace babu shakka kungiyar tana da hanyar samun kudi, idan ba haka ba da tuni ta salwance. Ya ce, “ganin cewa su na iya samun mayaka, da horas da su da samar musu da makamai, lallai su na da wata hanyar samun kudin gudanar da kungiyarsu.”

Orji ya ce yana da matukar wuya a san takamammen wanda ke samarwa da kungiyar kudade, domin babu wani cikakken bayani game da wannan kungiya ko yadda take samun kudaden. Yace idan har hukumomin leken asirin Najeriya sun san wanda yake ba kungiyar kudade tana tawaye, to ba su sanar da duniya ba.

Abinda kawai ya bayyana shi ne cewa irin ayyuka da hare-haren Boko Haram a wannan lokaci, sun rikide sun koma na kwararru fiye da lokacin da kungiyar ta fara tayar da kayar baya a shekarar 2009, daga lokacin da aka kashe dubban mutane.

Darektan wata cibiya mai suna “Policy and Legal Advocacy Center” a Abuja, Clement Nwanko, yace tana yiwuwa Boko Haram tana samun kudaden gudanar da ayyukanta ne daga kungiyoyin kishin Islama dake kokarin samun cibiya a Afirka ta Yamma.

Mr. Nwanko yace, “ina jin cewa akwai wani kudin dake shiga musu daga wasu kungiyoyin kishin addini, daga kungiyoyin da watakila su na son su samu sansani a arewacin Najeriya.”

Wani tsohon kyaftin na soja kuma mai bayarda shawara a kan harkokin tsaro, Aliyu Umar, yace sanin yadda kungiyar take samun kudadenta yana da wuya a yanzu, kuma rundunar sojoji su na bukatar kara kaimi wajen ayyukan leken asiri domin ganowa. Yace idan har za a iya gano yadda suke samu, to ana iya toshewa.

Mr. Nwanko dai yace a yanzu akwai hanya guda da aka sani ta yadda Boko Haram take samun kudade, koda yake sabuwar hanya ce. Yace duk da cewa satar mutane da yin garkuwa da su domin kudin fansa ba shi ne ya kirkiro da tasirin kungiyar ba, a yanzu yana taimaka mata wajen kara yin karfi.

A wannan shekara, an sace ‘yan Najeriya da dama domin neman kudin fansa daga iyalansu. Kamfanin dillancin labaran reuters yace ya ga takardun da suka nuna cewa an biya kungiyar Boko Haram sama da dalar Amurka miliyan uku domin sako wasu Faransawa da ta kama.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG