Wadannan jihohi sune Borno, Yobe da Adamawa, kuma yau kwanaki 10 tun bayan kaddamar da dokar, kuma hakan ya zone da da katsewar duka hanyoyin sadarwa ta wayar tarho a mafi yawancin wadannan jihohi.
Dakarun Najeriya sun katse layukan wayoyin ne domin kaddamar da hare-hare kan ‘yan kungiyar nan ta Jama’atu Ahlil Sunna Li Da’awa wa Jihad da ake kira Boko Haram.
An Katse layukan wayoyin ne bayan da dakarun Najeriya suka fara isa yankunan arewa maso gabashin Najeriya dake kusa da kasar Nijar, Kamaru da Cadi.
A dai-dai lokacin da dakarun Najeriya ke yunkurin kwato wasu sassan jihohin Borno, Yobe da Adamawa, jin ta bakin wasu daga cikin mutanen wadannan jihohi yayi wahala, kuma ma wasu mutanen kamar wani mutum da baya so a fadi sunansa.
“Tun tahowa na daga Damaturu, ina ta neman wayan iyalaina, ban same su ba, ina ta neman wayan abokaina da sauran ‘yan uwana.” Inji wannan mutum kennan da yake ganawa da wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Mohammed.
Wani manomi kuwa, ya alaqanta katse layukan waya da zalunci. A ganinshi, hanya ce da dakarun Najeriyan ke amfani da ita wajen cin karensu babu babbaka.
Jihar Borno itace tungar kungiyar da ake kira Boko Haram, kuma anan ne aka fara wannan rigima tun shekara ta 2009 bayan da ‘yan sandan Najeriya suka kashe wasu ‘ya’yan kungiyar, da shugaban kungiyar Muhammad Yusuf a fili ba tare da shari’a ba. Wannan ya fusata kungiyar, shine suka dauki makamai suka fara kaiwa dakarun tsaro, sojoji da gidajen Yari hari a duk fadin arewacin Najeriya.