“Suna so sub a kasashe tsoro, su razana kasashe sosai, domin su ci karensu babu babbaka. Shi fada, da yaki dan yaudara ne, in ka bari, sai a yaudare ka, a yi maka zamba.” A cewar Farfesa Ado Muhamman.
Ra’ayoyin sun bam-bamta. Malam Muhammadu Juri na wata kungiyar fararen hula yace dole sai an sauya salon siyasa a Nijar sannan za’a iya kiyaye irin wadannan hare-hare.
A jiya Alhamis ne wasu motoci dankare da bama-bamai sun tarwatse a mashigar barikin sojan garin Agadez da garin Arli, inda mutane kimanin 20 su ka riga mu gidan gaskiya, baya ga da dama da su ka sami raunuka.
Kungiya mai tsatsaurar ra'ayin Islama, MUJAO a takaice, ita ce ta dauki alhakin wannan hari.