Dakarun burged ta 1 ta rundunar karta kwana dake shiya ta 2, dake aikin wanzar da zaman lafiya mai taken “Operation Fansan Yamma, sun hallaka wani kasurgumin dan ta’adda a jihar Zamfara.
An hallaka Alhaji Ma’oli tare da wadansu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a jiya Alhamis.
Jami’i mai kula da cibiyar yada labaran, aikin wanzar da zaman lafiyar na fansan yamman, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, yace samamen da ya kai ga kisan Alhaji Ma’oli da sauran ‘yan ta’addar ya faru ne a kauyen mai sheka kusa da garin Kunchin Kalgo “wanda ya kasance daya daga cikin garuruwan yankin da suka sha wahalar ta’addancin Ma’oli”.
“Ma’oli ya yi kaurin suna a kan kakabawa mazauna garuruwan Unguwar Rogo da Mai Sheka da Magazawa da ma kauyukan da ke kewayen garin Bilbis na karamar hukumar Tsafen jihar Zamfara haramtattun haraji,” a cewar sanarwar da Abdullahi ya fitar a yau Juma’a.
A cewarsa, mutuwar Ma’oli ta haifar da kwanciyar hankali da annashuwa ga al’ummar Bilbis da kewaye.”
Ya kara da cewa samamen ya biyo bayan samun rahotannin sirri game da ayyukan ‘yan ta’addar da ke kan babura da suka addabi yankin Bilbis, na karamar hukumar tsafen jihar Zamfara.
Dandalin Mu Tattauna