Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 4 Da Suke Zargi Da Daukar Nauyin Ayyukan Ta’addanci A Katsina


Nigeria Police Force Logo
Nigeria Police Force Logo

An kama wanda ake zargin ne yayin sintirin yau da kullum akan babbar hanyar ‘Yan Tumaki zuwa Kankara a ranar 19 ga watan Nuwamban daya gabata a karamar hukumar Danmusa ta jihar.

Jami’an rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina sun kama wani da suke zargi da daukar nauyin ayyukan ta’addanci, Aminu Hassan, a bisa zarginsa da agazawa ‘yan bindigar da suka addabi karamar hukumar Danmusa da kewayenta.

Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana hakan a sanarwar daya fitar a jiya Talata.

Yace wanda ake zargin mai shekaru 25 ya fito ne daga kauyen Dundubus na karamar hukumar Danja ta jihar.

Ya ci gaba da cewa kamen wani bangare ne na nasarar da rundunar ta samu a yakin da take yi da ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

An kama wanda ake zargin ne yayin sintirin yau da kullum akan babbar hanyar ‘Yan Tumaki zuwa Kankara a ranar 19 ga watan Nuwamban daya gabata a karamar hukumar Danmusa ta jihar.

An ce mutumin na dauke da khakin soja guda 2 da aka boye a cikin bakar jakar leda.

A yayin gudanar da bincike, an kama karin wadanda ake zargi da hannun a lamarin da suka hada da (1) Lawal M. Ahmad, mai shekaru 29 dana (2) Isma’il Dalhatu, mai shekaru 24, dukkaninsu daga Unguwar Basawa, ta karamar hukumar Sabon-Garin Zariya a jihar Kaduna da (3) Shafi’u Adamu, mai shekaru 28, daga kauyen Danjaba, a karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG