Duk kalaman da mahukunta ke yi a kan cewa ana samun saukin matsalolin rashin tsaro saboda ana kan samun galaba a kan 'yan ta'adda, har yanzu akwai al'ummomin da ke ci gaba da shan ukuba daga hannun 'yan bindigar.
Yanzu haka al'ummar garin Dan tudu dake Lajinge a karamar hukumar Sabon Birni dake gabashin Sakkwato na ci gaba da jimamin mutane tara da suka rasa rayukan su a hannun harin na 'yan bindigar.
Wani mutumin garin da ya samu tsira daga harin ya shaidawa wakilin muryar Amurka cewa, da ma mutanen garin sun samu labarin cewa akwai yiwuwar 'yan bindiga na kan hanyar kai hari a garin, yace mutane 10 ne ‘yan bidigar suka harba, tara sun mutu daya kuma an garzaya da shi a asibiti domin ceto rayuwar sa, sannan kuma sun yi garkuwa da matan mutanen da suka kashe.
Shugaban karamar hukumar Ayuba Hashimu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya da yake shaidawa wakilin muryar Amurka. Haka zalika shima Mataimaki na Musamman kan lamura a Karamar hukumar Malam Muhammad Lawal ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Jami'in mashawarci kan tsaro a karamar hukumar ya bayyana cewa an kashe mutanen ne ta hanyar harbi da bindiga a wuya.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da mahukunta a jihar da ma na tarayyar Najeriya ke cewa ana samun nasara a kan 'yan bindiga, inda bai kai wata biyu ba da ministan kasa a ma'aikatar tsaron Najeriya Bello Muhammad ya ziyarci yankin na gabashin Sakkwato tare da bai wa al’ummar yankin tabbacin samar da saukin kan rashin tsaro.
Wani mazaunin karamar hukumar ta Sabon Birni ya bayyana cewa babu wani sauki da aka samu akan matsalar tsaro domin har yanzu 'yan bindiga na cin karen su babu babbaka a wasu yankuna.
Duk da yake a kwanan baya an samu rahotannin cewa, Jami'an tsaro na tafka fada da 'yan bindiga, kuma jami'an tsaro na sa kai da 'yan banga na iya kokarin su, matsalar a iya cewa ta zamo kashin bakin tulu a gabashin jihar ta Sakkwato.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna