Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sake Dasa Nakiyoyi Kan Hanyar Zamfara


Yan bindiga
Yan bindiga

A yau Laraba, ‘yan bindiga suka dasa jerin sabbin nakiyoyi a yankin Mai Lamba na babbar hanyar Dansadau zuwa Gusau dake karkashin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, inda suka hallaka matafiya.

Sanarwar da jami’in yada labaran rundunar hadin gwiwar dake aikin wanzar da zaman lafiya mai taken Fansar Yamma, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya fitar ta tabbatar da afkuwar lamarin.

“Muna tabbatar da rahoto game da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka dasa nakiyoyi a kan hanyar Dansadau zuwa Gusau, wanda aka yi rashin sa’a ya haddasa barna.

Ya kuma bukaci al’umma su zamo masu sa idanu tare da kai rahoton duk wani motsi da basu yadda da shi ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG