Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Saman Najeriya Sun Yi Luguden Wuta Kan 'Yan Bindiga a Kebbi Da Zamfara


Rundunar Sojojin Saman Najeriya Na Ci Gaba Da Kai Hare Hare kan Yan Ta'addan
Rundunar Sojojin Saman Najeriya Na Ci Gaba Da Kai Hare Hare kan Yan Ta'addan

Hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya ta yi karin haske kan wasu tagwayen hare-hare da jiragen yakinta su ka kai kan gungun wasu yan bindiga a kan iyakokar jihohin kebbi da zamfara.

Tun da farko dai 'yan bindigar, kamar yadda wata majiya ta shaidawa VOA, sun taru ne a kauyen Madada da ke cikin yankin karamar hukumar Maru da nufin kai harin ta'addanci a wasu yankunan jihar kebbi.

Bayan da 'yan ta'addan suka sami labari sojojin kasa sun masu kwanton bauna ne kuma su ka juyo, inda kuma wasu jiragen yakin kasar suka yi masu ruwan wuta.

Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet ya shaidawa muryar Amurka cewa ba shakka sun hallaka dandazon yan bindiga masu yawan gaske, duk da yaki ya bayyana ainihin adadin wadanda su ka hallaka.

Ya ce ba kome suke bayyanawa a fili haka sakaka ba, amma dai harin ya sami cikakkiyar nasara sosai.

Mutanen da ke wannan yanki kuma tuni suka nuna farin ciki bisa yadda suka ce a baya-bayannan jami'an tsaron na taka rawar gani sosai, inda suka yi fatan hakan zai ci gaba.

Rundunar sojojin saman ta ce tana da kwarin gwiwar wannan hari zai taimaka gaya wajen kara dakile kaifin aika-aikar yan bindigar.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG