‘Yan awaren da ke fafutukar neman ballewa daga Najeriya su kafa kasar Biafra da ake kira IPOB a takaice da kuma mayakan ESN sun tsara kai hare-hare kan jama’a a daidai lokacin da Najeriya zata yi bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai nan da yan kwanaki masu zuwa, a cewar wasu rahotanni.
A wani mataki na tabbatar da tsaro, jiragen yakin mayakan saman Najeriya na rundunar “Operation Udoka,” sun fara kai hare-hare kan sansanonin da ‘yan awaren ke boye makamai a wasu dazukan da ke yankin gabashin Najeriya.
Kakakin hedkwatar rundunar mayakan saman Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce an samu nasarar kai hare-haren ne da hadin gwiwar dakarun kasa da na sama a sansanonin ‘yan awaren da ke dazukan jihohin Imo da Anambra.
Gabkwet ya ce sun sami bayanan sirri game da shirin da ‘yan awaren ke yi na kai farmaki a lokacin bikin zagayowar ranar samun ‘yancin Najeriya ranar daya ga watan Oktoba, shi ya sa suka fara daukar mataki don kare al’umma kuma sun sami nasarar kone tarin makaman da ‘yan awaren suka boye a dazukan yankin.
Mai sharhi kan sha'anin tsaro Dr. Abubakar MS, wanda ke bibiyar ayyukan mayakan, ya yaba da hadin gwiwar sojojin a kokarin da suke yi na wanzar da zaman lafiya, duba da irin barnar da ‘yan awaren ke tafkawa a yankin kudu maso gabas.
Wasu mazauna yankin na kudu maso gabas na fatan ire-iren wadannan farmakin na soja zasu dore har sai an kawo karshen kalubalen tsaro da ya addabi yankin.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina:
Dandalin Mu Tattauna