Makasudin taron shi ne don tattaunawa game da yajin aikin da malaman jami'o'i ke cigaba da yi da kuma fadakar da jama'a. Tsohon ministan albarkatun kasa na Nijeriya Farfasa Tom David West na daya daga cikin waddanda suka halarci taron. Ya ce yakamata gwamnatin Nijeriya ta bada ilimin jami'a kyauta. Ya ce ya kamata ta yi koyi da kasashen Ghana da Uganda da Afirka Ta Kudu wadanda na bada kashi ashirin da biyar na kasafin kudadensu ga harkokin ilimi.
Shugaban kungiyar malaman jami'a reshen Ibadan Dr Olusegun Ajiboye ya ce sun shirya taron ne domin su ilimantar da jama'a game da abubuwan dake faruwa dalilin yajin aikin. Ya ce baiwa sashen ilimi isasshen kudi yakamata ya zama abun da ya damu kowa da kowa. Shi kuma shugaban kungiyar kwadago ta jihar Oyo ya ce ya lura da damuwar kungiyar malaman jami'a da rashin isasshen kudi da wahalar da dalibansu ke sha. Shugaban wata kungiyar ma'aikata Kwamred Erubami ya ce yakamata gwamnati ta fahimci cewa samarma mutane ilimi zai bunkasasu.
Hassan Umaru Tambuwal nada rahoto daga Ibadan.