Hadarin ya kuma yi sanadiyar jakkatar mutane da dama tare da konewa wadansu motoci.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Naija, Mallam Ibrahim Hussaini yace tuni aka binne wadansu gawarwakin a inda abin ya faru, yayinda ake kulawa da wadanda suka yi mummunan rauni a asibiti.
A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari, Mallam Hussaini ya bayyana cewa, an yiwa mutane takwas jana’izar bai daya, aka kuma kai ishirin da daya asibitin Bidda inda ake yi masu jinya kyauta.
Masarautar Lapai ta nuna juyayin rashin ta kuma sanar da shiga zaman makoki. Mai martaba Umar Tafida Bago ya bayyana jimaminsa ya kuma ce sun gargadi matasa da su rika nisantar wuraren da aka sami hadari domin bada dama a kai agajin gaggawa.