Manufar kotun shi ne ta hukunta wadanda ake zargi da aikata munanan laifuffukan yaki daga duka bangarorin biyu, sakamkon yakin basasar da kasar tayi fama da shi na tsawon shekaru biyu.
Duk da cewa kafa irin wannan kotun yana cikin sharuddan yarjerjenoiyar zaman lafiya da duka shugabannin biyu suka sanya hannu kai. Saboda haka wanan makala ta janyo cecekuce a cikin kasar.
Amma kakakin shugaba Salva Kiir,ya kare makalar, yana mai cewa, kafa wannan kotu zai zake maida kasar cikin tarzoma.
Amma wani dan rajin kare 'yancin Bil'Adama Edmund Yakani, yace makalar wani yunkuri ne da wadanda suka aikata laifuffukan yaki kuma suke cikin gwamnati suke dauka domin kaucewa hukunci. Yace muddin ba'a hukuntasu ba za'a ci gaba da karya doka.