Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan jarida na fuskantar barazana ga aikinsu da rayuwarsu a Sudan ta Kudu


Oliver Modi, shugaban kungiyar 'yan jarida ta kasar Sudan ta Kudu
Oliver Modi, shugaban kungiyar 'yan jarida ta kasar Sudan ta Kudu

Jiya Talata da aka yi bikin ranar 'yan jarida ta duniya rahotanni sun nuna cewa Sudan ta Kudu ita ce kasa ta 140 cikin 180 a duniya kan 'yancin aikin jarida musamman wurin neman tantance labari daga jami'an gwamnati

Jiya Talata ce ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya, Sudan ta kudu ce kasa ta 140 cikin kasashe 180, bisa rahotannin kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa da ake kira Reporters without Borders. 'Yan jarida a kasar suka ce ba ma kawai aikinsu yana tattare da kalubale ba, amma rayukansu sukan zama cikin hadari idan suka nemi tace gaskiya. 'Yan jarida basu da sukunin samun bayanai daga hukumomin gwmnati, kuma anci zarafn wasu 'yan jarida masu yawa, har ma wasu mutane da ake jin jami'an gwamnati ne, su tsare su na makonni.

Masu kade-kade da raye raye suka kayatar a wani gangami da aka yi a birnin Juba jiya Talata, domin karrama wannan rana. A taron 'yan kasa da wasu 'yan jarida sun duba irin muhimmiyar rawar da 'yan jarida suke takawa a Sudan ta Kudu, da kuma haska fitila kan cin zarafin manem labarai.

XS
SM
MD
LG