Hukumomin bada agaji ta Majalisar dinkin duniya, sunce rikicin da kasar Sudan ta Kudu ke fama dashi hadi da yanayin da kasar take cikin a halin yanzu ya taimaka wajen raguwar samun albarkatun noma.
Hukumar abinci da ayyukan noma ta Majalisar dinkin duniya, da hukumar samar da abinci albarkatun noman alkama da aka saba samu ya ragu da a kalla kashi 53 idan aka kwatanta shi da abinda kasar ta samu a shekarar data gabata.
Hukumar yace wannan halin da kasar ta samu kanta cikin kara taazzara matsalar da kasar ke fuskanta na rashin abinci.
Haka kuma wannan ya biyo bayan rahoton da hukumar ta bada agaji tace yawancin gidaje suna rayuwa ne ta cin abinci sau daya a rana domin kayayyakin abinci sunyi tashimn gwauron zabi.
Shugaban kula da hukumar abinci ta Majalisar dinkin duniya, ta Sudan ta Kudu Bernard Owadi yace ana sa ran al’amarin ya kara muni domin ko nan bada jimawa ba farashin abincin zai karu da kusan ninki hudu ko fiye a cikin ‘yan watanni masu zuwa.
Yanzu haka dai ‘yan kasuwa basu iya shigo da wadannan kayayyakin abincin daga kasashen waje kamar yadda suke yi ada, domin suna samu matsalar yin hakan akan hanyar su ta shigowa dashi cikin kasar.