Bangarorin biyu sun yi zaman ne a Juba, babban birnin kasar ta Sudan ta Kudu a jiya Talata, da fatan za a kafa gwamnatin wucin gadi, wadda za ta kunshi dukkanin bangarorin da ke takaddama.
A baya ‘yan tawayen da gwamnatin sun sha gudanar da zama, tun bayan da yakin basasan ya barke a tsakiyar watan Disamban shekarar 2013, sai dai an yi ta saba yarjeniyar tsagaita wuta da aka samar a shekarun biyun da suka gabata.
Shugaban Salva Kiir da shuagban ‘yan adawa Riek Machar, sun sha zargin juna da saba yarjeniyar zaman lafiya, amma dukkaninsu suna ikrarin cewa za su ci gaba da mutunta yerjeniyar 26 ga watan Agusta da aka kulla, duk da cewa ana saba wa’adin da aka cimma.
Sudan ta Kudu, ita ‘yar autar kasashen da suka samu ‘yan cin kai a duniya, bayan da ta balle daga Sudan a shekarar 2011.
Dubun dubatar al’umar kasar wannan rikici dai ya halaka, kana ya raba mutane miliyon biyu da muhallansu.