Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka


Donald Trump zababben shugaban kasar Amurka na 47
Donald Trump zababben shugaban kasar Amurka na 47

Zaben ya nuna cewa Donald Trump ya doke mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris, da kuri’u sama da yadda aka yi hasashe, yayin da Trump ya samu rinjayen kuri’u wakilan jihohi sama da 270 da ake bukata.

An dai zabi tsohon shugaban Donald Trump a matsayin sabon zababbaen shugaban Amurka na 47.

Jama'ar Ghana kamar sauran kasashen duniya, sun bibiyi zaben yayin da Donald Trump ya fito a matsayin wanda ya yi nasara, kuma masu sharhi da wasu ‘yan Ghana sun bayyana ra’ayinsu game da zaben.

Nasara da Donald Trump ya yi a wannan zaben bai bai wa wasu mamaki ba domin ya bayyana manufofinsa karara ga al’ummar Amurka.

Maryam Bawa, ‘yar jarida mai zaman kan ta ta ce, manufofin na sa kuma sun dace da wadanda ‘yan Amurka suke bukata.

“Ni a nawa tunanin, ya iya ya fito da manufofinsa ne, ya iya ya fitar da su yadda ya kamata. A duk lokacin da ya zauna ake tattaunawa da shi, ba abinda yake mai da hankali a kai sai yadda kasar Amurka za ta samu ci gaba. Kuma wadannan bayanai da yake yi, zai sa mutane da dama da za su yi ra’ayi da shi.”

Wani ba’amurke dan asalin Ghana da ya bibiyi zaben a Ghana, Umaru Braimah ya ce, shi da ya so Kamala Harris ta lashe zaben, amma tun lokacin da aka fara yakin Isra’ila da Falasadina kuma gwamnatin Biden da Kamala suka marawa Isra’ila baya ba tare da tausayawa abin da ke faruwa ga al’ummar Falastin ba, ya ga alamun cewa lallai Kamala za ta fadi zaben.

Umaru Braimah ya kara da cewa, yadda bayan sa karaya daga bangaren tawagar Donald Trump, musamman kan bakin hauren baki ya taimaka masa wurin nasarar da ya yi, domin batun, lamari ne da jama'ar Amurka ke kuka da shi.

Yunus Swalahudeen Wakpanjo, mai sharhi kan harkokin yau da kullum ya yi kira ne ga sabon shugaban cewa, idan an rantsar da shi, to ya waiwayi wasu matsalolin hulda tsakanin kasa da kasa da kasar Amurka ke fuskanta da wasu kasashen duniya. Ya ce, Trump ya yi duba da idon basira kan lamarin bakin haure.

Duk da cewa an gudanar da zaben wuri a Amurka, amma tsakanin jiya (Talata) zuwa yau (Laraba), miliyoyin Amurkawa suka kada kuri’a kuma aka samu sakamako cikin awa 24 haka.

Bangaren da Alhaji Garba Osman ya mayar da hankali ke nan, inda ya ce lallai akwai abin kwaikwayo ga Ghana daga wannan tsari na Amurka, sai dai ya yi wuya a iya cimma wannan burin na ba da jimawa, domin Amurka ta fara dimokradiya fiye da shekaru 200, amma “Idan muka tsaya turban dimokradiya, da yardan Allah mu ma za mu samu hakan.”

Za a dai rantsar da shugaba Trump a ranar Litinin 20 ga watan Janairun 2025.

Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah:

Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Akan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG