Dukkan ‘yan takarar biyu sun yi nasarar lashe zaben tun da wuri a wasu jihohi dake zaman tungarsu a zaben mai cike da tarihi da ka iya ganin Amurka ta zabi shugabar kasa mace ta farko.
Trump, wanda ke neman komawa fadar White House bayan ya sha kaye a shekarar 2020, ya kwace jiharsa ta Florida, inda ya samu wakilai 30 na jihar. Harris, kamar yadda aka zata, ya samu nasara a kananan jihohi masu yawa a Gabashin Amurka.
Dan takarar da zai lashe zaben na bukatar wakilai 270 daga cikin 538 domin ya samu nasara, kuma ba a sa ran wasu jihohin za su kammala kidayar kuri’u kafin ranar Laraba. Wanda ya yi nasara zai fara wa'adin shugaban kasa na shekaru hudu a watan Janairu.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun yi hasashen cewa kallo zai koma kan jihohi bakwai ne kacal a fagen siyasa, inda bincike ya nuna 'yan takarar biyu na tafiya kankankan da juna - wanda hakan ya sa ake ganin mai rabo ne kawai zai samu.
Dandalin Mu Tattauna