Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Yawancin Rumfunan Zabe A Fadin Amurka


Zaben Amurka
Zaben Amurka

Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris na da wakilai 179 na zabe, yayin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya samu wakilai 214.

Harris ta sami nasara jihohin California da Washington da kuma Washington, D.C. da jihar Maine. A halin da ake ciki, Trump ya lashe jihohin Idaho da Iowa da kuma Kansas.

Yanzu haka dai an rufe akasarin rumfunan zabe a kasar. Sun rufe rumfunan da karfe 11 na dare lokacin gabashin Amurka, a jihohin California da Idaho da Oregon da kuma Washington, kuma ana shirin rufewa a wasu jihohin da karfe 12 na tsakar dare, wanda yake daidai da agogon Hawaii da karfe 1 na dare a jihar Alaska.

Ana ci gaba da kidayar kuri'u a muhimman jihohin Wisconsin da Michigan da Pennsylvania da Jojiya da kuma Arizona. Kamar yadda aka yi hasashe, zaben zai kasance kankankan, a cewar Elaine Kamarck, babbar jami'a a cibiyar Brookings.

Ta ce “Zai sauko zuwa wasu tsirarun jihohi,” kamar yadda ta shaidawa Muryar Amurka.

A fafatawa a zaben ‘yan Majalisar Dattawan Amurka, jihohin Maryland da Delaware sun kafa tarihi a daren jiya Talata, inda suka zabi ‘yan jam’iyyar Democrat Angela Alsobrooks da Lisa Blunt Rochester a matsayin ‘yan majalisar dattawa. Wannan dai shi ne karon farko da mata biyu ‘yan jam’iyyar Democrat, za su yi aiki a majalisar dattawa a lokaci guda.

“Daga cikin zuciyata, ina godiya ‘yan jihar Delaware" in ji Rochester a cikin wani sakon da ta wallafa a dandalin sada zumunta na X.

A wani wuri na daban a zaben ‘yan Majalisar Dattawa, Tim Kaine na Virginia da Martin Heinrich na New Mexico, dukkansu 'yan Democrat, sun sake lashe zaben.

Ga 'yan Republican, Ted Cruz daga Texas da Josh Hawley daga Missouri, duk sun sake lashe zaben. John Curtis dan Republican shima ya lashe zaben sa na Majalisar Dattawa a Utah.

Batun zubar da ciki ya kasance a kan katin jefa kuri'a a jihohi 10 a wannan zagayen zaben.

Mazauna birnin New York sun kada kuri'ar amincewa da matakin da aka tsara don kiyaye kariya ga zubar da ciki. Amma a Florida, mazauna yankin sun yi watsi da yunkurin soke dokar hana zubar da ciki na mako shida na jihar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG