ACCRA, GHANA - Shugaban ya ce wasu kasashen na Yamma na da hannu a juye juyen mulki da ke faruwa a sassan nahiyar Afirka. ya ce suna hakan ne domin cimma manufofinsu.
Shugaban na Ghana ya fadi hakan ne a taron kwana uku na kungiyar AE tare da hadin guiwar gwamnatin Ghana a birnin Accra inda taron ya maida hankali akan juye juyen mulki ba kan ka’ida ba da nahiyar ke fama da ita.
Ya ce suna kushe gwamnatocinsu da aka kafa ta dimokradiyya tare da cusa wa al’ummar kasashen akidar aiwatar da zanga-zangar adawa da gwamnati.
Shugaban ya kuma tabo matakan da AU da ECOWAS din ke dauka na yin Allah wadai da juyin mulki, ya ce hakan kadai ba zai haifar da wani alheri ba sai dai idan aka dauki matakan ladabtar da wadanda suka jagoranci juyin mulki.
Ya kuma kara da cewa kungiyoyin na AU da ECOWAS ya kamata su ladabtar da shugabannin da ke yi wa tsarin mulki kwaskwarima domin yin ta zarce.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti daga Hamza Adams: