NIAMEY, NIGER - Tuni dai Shugaba Mohamed Bazoum ya ayyana shirin daukan matakai don kawo karshen wannan dabi’a dake bata sunan Nijar a waje.
Mamayar da wasu ‘yan Nijar suka yi wa titunan Dakar na kasar Senegal a makwannin da suka gabata ita ce mafarin dambarwa da ta taso a tsakanin jama’ar wannan kasa dake ganin lokaci ya yi da za a taka burki ga masu fita waje da sunan bara, ganin yadda abin ke wuce gona da iri.
Shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula na Reseau Esperance Bachar Maman na daga cikin masu ciza yatsa akan wannan batu.
Dama daga cikin masu rungumar wannan kaskantacciyar dabi’a na fakewa da addini don mayar da ita sana’a wadan da galibi kan yi abin ba da wata kwakwarar hujja ba, wannan ya sa malamai magada annabawa irinsu Ustaz Malan Haja Alalo suka fara tunatarwa a musulunce.
Wani abinda ke zama bakon al’amari shine irin yadda ake amfani da yara kanana cikin wannan haraka.
Gudunmowar al’umma a yunkurin cire bara daga kawunan wadanda suka mayar da ita sana’a na iya zama wani bangare na matakan murkushe abin tun daga gida.
Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum wanda a karshen watan Maris ya bada umurnin maido da wasu ‘yan Nijar sama da 1000 akasarinsu mata da yara dake bara a kasar Senegal ya lashi takobin kawo karshen wannan haraka.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: