Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Nijer Ya Ce An Samu Ci Gaba Ta Fannin Tsaro Cikin Shekara Daya Na Mulkinsa


Hotunan Rantsar Da Bazoum Mohamed A Matsayin Sabon Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar
Hotunan Rantsar Da Bazoum Mohamed A Matsayin Sabon Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar

A yayin da a ranar biyu ga watan Afrilu ya cika shekara daya da dare karagar mulki, shugaban kasar Nijer ya bayyana samun nasarori a fannin tsaro a yankunan da ke fama da aiyukan ta’addanci.

YAMAI, NIJER - A wani taron manema labarai da ya kira a birnin Yamai ne Shugaban Nijer Mohamed Bazoum ya bayyana nasarorin da ya samu a cikin shekara daya na mulkinsa.

Ko da yake, shugaban ya ce har yanzu da sauran rina a kaba saboda haka zai ci gaba da hada gwiwa da takwarorin aikinsa na kasashe makwafta domin kawo karshen tashe tashen hankulan da suka tilasta wa dubban mutane tserewa daga garuruwansu na asali.

Shugaba Bazoum ya ce a tsawon watanni shabiyu na mulkinsa an samu sauyi a jihar Diffa, inda gwamnatinsa ta fara maida ‘yan gudun hijirar cikin gida zuwa garuruwansu na asali kuma zai ci gaba da wannan aiki don ganin dukkan irin wadannan mutane sun koma gida kafin daminar da ke tafe.

"Gwamnan jihar Borno shi ma ya fara kwashe al’umarsa da ke hijira a Nijer. Wannan ma ci gaba ne," a cewar shugaban.

Mohamed Bazoum ya kuma ce a jihar Tilabery al’amura sun lafa domin ko a baya bayan nan hukumomi sun shirya wani taron sulhunta kabilun yankin da ke fama da rikicin cikin gida, to sai dai kasancewar ‘yan ta’adda sun tare akan iyakar Nijer da Burkina Faso ya sa aka tsaurara matakai inda dakarun tsaro ke sintiri. Shugaban ya kuma jinjina wa sojojin Nijer tare da gode musu da addu’ar Allah ya basu sa’a.

A yankin jihar Maradi, duk da yake an samu ci gaba, yanzu kuma ana kara samun kwararowar ‘yan gudun hijira sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro a wasu jihohin Najeriya. A saboda haka ne gwamnatin Nijer ta fara tattaunawa da gwamnonin jihohin da ke fama da aika aikar ‘yan bindiga don samo bakin zare, a cewar Bazoum.

Saurari cikakkiyar hirar Souley Mumuni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG