A karshen ziyarar da ya kai a ranar 31 ga watan janerun da ya gabata a kasar Mali Firai Ministan rikon kwaryar Burkina Faso Apolinaire jaochim kyelem de Tambela ya bullo da shawarar kafa hadakar federaliya a tsakanin kasashen 2 masu matsaloli iri guda.
Haka kuma a wani taron da suka gudanar a birnin Ouagadougou a ranar 9 ga watan nan na fabreru ministocin harkokin wajen Burkina Faso da na guinea da na Mali sun sake nanata wannan aniya da nufin tunkarar kalubalen da ke gabansu.
Sai dai da yake maida martani a taron cikon shekara 1 da juyin mulkin da ya kawar da Alpha Conde daga karaga mataimaki na 2 na shugaban Majalisar ECOWAS, Boukari Sani Zilly yace ba za su laminta da irin wannan take take ba dake barazanar haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen yammacin Afrika.
Shugaban kungiyar farar hula ta MOJEN Siraji Issa ya yaba da matsayin Majalissar ta CEDEAO.
A ra’ayinsa wannan yunkuri hujja ce da ke nunin sojojin dake mulki a wadanan kasashe ba su da niyyar shirya zaben da zai mayar da mulki a hannun fararen hula.
To amma wani mamba a kungiyar M62 Gamatche Mahamadou na ganin rashin dacewar tsoma bakin Majalissar ta ECOWAS a sha’anin cikin gidan wadanan kasashe da ya kira masu fafutikar kubutar da kansu daga turawan mulkin mallaka.
A nan dan Majalisa Boukari Sani ya yi tunatarwa kan yarjejeniyar protocole additionnel da kasashen CEDEAO suka rattaba wa hannu a shekarar 2001 .
Burkina faso , da Mali, da Guinea Conakry na fama da takura a sakamakon dakatarwa daga kungiyar ECOWAS saboda juyin mulkin da soja suka yi a kasashen 3 wadanda a halin yanzu suka raba gari da kasar da ta yi masu mulkin mallaka wato Faransa, hujjoji masu karfi na nunin kusanci a tsakaninsu da Russia da suke dauka a matsayin sabuwar uwar daki.
Saurari rahoton a sauti: