Jami’an kwamitin dai basu ji dadin ganawar da sukayi da shugaban kasa Pierre Nkurunziza a jiya Juma’a ba, saboda bai nuna musu wata alama da take nunin zai iya canza zuciyarsa ya karbi sojojin kiyaye zaman lafiya da kungiyar tarayyar Afirka ta AU ke kokarin aikawa kasar, ko neman a zauna teburin sulhu da ‘yan adawa.
Wakiliyar Amurka a MDD Samatha Power ta fadawa manema labarai cewa, “Dole ne Kungiyar Tarayyar Afirka, ta san mataki na gaba da zata ‘dauka, tunda dakarun da ta amince zata aika anki karbarsu.” Ta fadi hakane bayan ganawarta da kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU.
Shugabannin Afirka zasuyi taron koli na shekara shekara cikin mako mai zuwa in Allah ya kaimu, hakan yasa jami’an diplomasiya sukace zasu saka ido domin ganin sakamakon taron na wannan shekara.