Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BURUNDI: Shugaban jam'iyyar adawa yace ana iya samun zaman lafiya


Shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron lalubo bakin zaren rikicin siyasar kasar Burundi
Shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron lalubo bakin zaren rikicin siyasar kasar Burundi

Shugaban Jam’iyyar adawa ta FRODEBU a kasar Burundi, da ke gudun hijra, ya ce yunkurin da ake yi na samar da maslaha kan rikicin kasar na nan bai mutu ba, saboda a cewar sa mutanen Burundi sun cancanci zaman lafiya.

Shirin zaman sasanta rikicin kasar da aka shata za a ci gaba da yi a ranar shida ga wannan wata na Janairu a Kampala, babban birnin Uganda bai yiwu ba, saboda gwamnatin Pierre Nkurunziza ta ce ba ta amince ta hau teburin tattaunawa da wasu ‘yan adawa da ta zarga da cewa “masu juyin mulki” ne da kuma “marawa ayyukan ta’addanci baya.”

Sai dai shugaban jam’iyyar ta FROBEDU, Jean Minani, ya ce shugaba Nkurunziza ya ambaci cewa ba za a yi watsi da tattaunawar ba.

Ya kuma kara da cewa, gwamnatin ta Nkurunziza ta kwan da sanin cewa, idan har ba za ta bi hanyar sasanta rikicin ba, to za a tilasta mata hawa teburin tattaunawar.

Minani ya kuma ce, ya kamata shugaba Nkurunziza ya san cewa sulhu irin wannan, ana yin shi ne tsakanin abokanan gaba, ba tsakanin aminai ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG