Shugaban kasar ya tura wani kwamiti zuwa jihar Arewa mai nisa, karkashin jagorancin gwamnan jihar, domin mikawa mutanen su shida gudummuwar abin masarufi.
An ba mutanen da suka shafe kwanaki dari biyu da goma sha uku a hannun kungiyar Boko haram gudummuwar ne domin su iya samun abin biyan bukata kafin su iya komawa gudar da harkokinsu na yau da kullum. Gwamnati ta ba mutanen tallafin jaka dari biyar kowannensu.
Kungiyar Boko Haram ta kama mutanen ne da misalin karfe goma na safe a kan hanyarsu zuwa garin Kuseri daga Marwa ta shiga da su jeji inda tayi garkuwa dasu na tsawon wadannan kwanaki kafin rundunar tsaron hadin guiwa ta ceto su.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Mohammed Awal Garba ya aiki daga Yaounde, Kamaru.