Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Kamaru


Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya

A cigaba da ketara kan iyakokin makwabtan kasashe su na aika-aika, 'yan bindigar Boko Haram sun wasu hare-hare a Kamaru. Na baya bayan nan shi ne na kunar bakin wake a wani masallaci.

Da asubahin jiya Litini wani dan kunar bakin wake ya kai hari cikin wani masallaci cike da masallata a Karamar Hukumar MayoMaskota da ke jahar Arewa Mai Nisa, inda ya hallaka mutane hudu lokacin da ya tarwatsa kansa a masallacin.

Idan ba a mance ba dai kwanan nan ne ma wasu hare-haren kunar bakin wake su ka yi sanadin mutuwar mutane 13 a garin Kuyape da ke Karamar Hukumar Kolofaka, kwana guda bayan da sojoji su ka kama wasu ‘yan kunar bakin wake hudu a Ashigashiya.

Alkaluma na nuna cewa ya zuwa yanzu, ‘yan Boko Haram kashe yaruka da dama, ciki da farar hula 1,100, sojoji wajen 67 ‘yansanda kuma 3.

Ga wakilinmu Muhammadu Danda da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG