Kungiyar ma'aikatan ta basu umurnin duk ma'akatan su shiga yajin aiki yau daga karfe tara na safe zuwa karfe shida na yamma.
Yajin aikin na nuna fushi ne ga gwamnati akan rashin samun tallafi kamar bayan da tayi masu akawarin miliyan dari uku na sefa. Tallafin zai zama diya ne bisa ga hasarar da suka tafka yayin wata tarzoma bara.
Abdulaziz Taya daya daga cikin kungiyar ma'aikatan yace basu san hawa ba bale sauka lokacin da rikicin ya barke sanadiyar rikicin kasar Faransa na Charlie Hebdo. Yace haka kawai aka kai hari kan wuraren da ake shakatawa ko shan giya do ma otel otel suka cinna wuta har ma ak akshe wasu..
Shekara guda ke nan suna bin gwamnati sau da kafa da ta cika alkawarin da ta dauka.
Ga karin bayani.