Ahalinda ake ciki kuma, shugaban Amurka Donald Trump, ya zargi mai bincike na musamman Robert Muller, da nuna son zuciya ta siyasa a cikin aikinsa na binciken ko akwai wata alaka tsakain kwamitin kemfen na Trump a zaben shekarar 2016, da Rasha, da kuma neman sanin ko shugaban na hana ruwa gudu ko yin murdiya ga aikin binciken.
Trump yace mai yasa kwamitin Muller ke aiki da rikakkun yan Democrat 13, wadanda aka san su cikakkun magoya bayan Hillary ne, amma kuma babu wani dan Republican ko daya. Yace a cikin wannan lokaci an kuma kara wani dan jam'iyyar Democrat daya, shin wannan adalci ne? Amma har iyau babu wata alaka hada baki da aka gano! Trump ya fadi haka ne a cikin daya daga cikin sakwanninsa na Tweeter a karshen mako, da yake tunawa da nasarar da ya yi a kan abokiyar karawarsa Hillary Clinton, da kuma yanda yake yiwa binciken kallon hadarin-kaji, da aka kwashe shekara guda da rabi ana gudnarwa.
Sai dai Trump kasa tuna cewa, a wani lokaci Muller cikakken dan jami’iyar Republican ne kuma a Amurka ana masa kallon lauyan da babu ruwansa da siayasa a aikinsa, wanda bincikensa a kan kemfen Trump ke samu goyon daga 'yan Democrat da wasu manyan yan Republican, wadanda suka bayyana goyon bayan su a kan yanda Muller yake gudanar da binciken, yayinda suka fito a wasu shirin labarai na jiya na talabijin a jiya Lahadi.
Facebook Forum