Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Dau Matakin Ramuwar Gayya Kan Amurka Tare Da Gargadi


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Da alamar za a bude wani sabon babi a rikicin Amurka da Rasha bayan da Rasha ta mai da martani saboda takunkumin da Amurka ta kakaba ma ta.

Rasha za ta kara yawan sunayen Amurkawan da za ta ladabtar, a martaninta kan takunkumin da aka kakaba ma wasu ‘yan Rasha da aka zarga da yin katsalandan a zaben Amurka.

Kamfanin dillancin labaran Rasha RIA Novosti, ya ruwaito Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Ryabkov na fada yau Jumma’a cewa, kasar Rasha na kan shirya takunkumin da za ta kakaba kan wasu da ta kira, “Ayarin sabbin Amurkawa masu wargi,” da kuma yiwuwar ta dau “karin matakai.”

Ryabkov ya zargi Amurka da yin barazana ga kwanciyar hankalin duniya, to amma ya ce burin Rasha shi ne cigaba da tattaunawa da Amurka, duk kuwa da daukar matakin ramuwar gayya da ya zama tilas gareta saboda abin da ta kira, “taurin kan Amurka a siyasance,” a cewar kafar labaran RIA.

Jiya Alhamis gwamnatin Trump ta bayar da sanarwar kakaba takunkumi kan wasu ‘yan Rasha 19 da kamfanoni 5, da ake zargi da shiga sharo-ba-shanu a zaben Amurka na 2016.

Amurka ta kuma bi sahun kasashen duniya wajen yin tir da Rasha, saboda kai hari da aka yi a Burtaniya da guba, wanda ake zargin Rashar ce da aikatawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG