Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Shiga Littafin Tarihi


Shugaba Trump da Shugaban Korea ta kudu
Shugaba Trump da Shugaban Korea ta kudu

Shugaba Donald Trump ya zama shugaban Amurka na farko da ya kai ziyara a Korea ta Arewa, inda ya taka ya tsallaka iyakar kasar, a lokacin da suke ganawa da shugaban korea ta Arewa Kim Jong Un a yankin da ba a gudanar da ayyukan soji.

Bayan ya yi hannu da shugaba Kim a kan iyakar dake kauyen Panmunjom, Trump ya taka ya ketara layin soji da ya raba tsakanin kasashen koriyoyin biyu. Bayan haka Trump da Kim sun tsallaka zuwa cikin Kortea ta Kudu.

Barka da sake ganinka, Kim yana fadawa Trump, yace bana tsammanin zan ganka a nan wurin.

Tsallaka wannan iyaka wani babban girmamawa ne, inji Trump wanda ya gayyaci Kim zuwa Amurka domin sake wata ganawa.

Trump ya fada a ranar Asabar cewa ganawar su ba zata wuce minti biyu ba. Sai dai tattaunawar da Trump ya kwashe mintoci hamin yana yi da Kim a sirrance ta zama tamkar wani taron koli.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG