A dai-dai lokacin da kasar Habasha ke shirin soma zaman juyayi akan abinda ofishin frayim-minista ya kira “yunkurin juyin mulki” da aka so a yi, ana ta ci gaba da yin tambayoyi gameda manufofin jagabannin yunkurin kifar da gwamnatin, musamman shi jagoran nasu.
A jiya Litinin ne dai kafofin watsa labaran gwamnati, suka bada sanarwar cewa an kama kuma an kashe wani babban hafsan soja mai suna Burgediya Janaral Asaminew Tsige, a lardin Amhara. Jami’an tsaro sunce an kashe shi ne yayinda yake kokarin ya gudu.
Shi dai wannan hafsan sojan sannane ne a ko ina a kasar Ethiopia, musamman da yake ya taba rike mukamin shugabancin Hukumar Tsaro ta yankin Amhara, kuma yana da goyon bayan dimbin ‘yan kabilar Amhara din.
Tun kafin zuwa yanzu, gwamantin tarayyar kasar ta sha zarginsa da laifin kitsa rikittan da suka barke har aka kai ga hallaka shugaban yankin na Amhara.
Facebook Forum