Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta amince da wasu canje-canje da gwanatin kasar ta aiwatar a kundin zabe, da ci gaba da shirye shiryen zabukan 2021.
'Yan adawa sun fita daga zauren majalisar a dai dai lokacin da aka fara muhawara akan wannan labarin, saboda a cewarsu matakin wata hanya ce ta shirya magudi.
Daukacin ‘yan majalisar na bangaren masu rinjaye ne suka amince da gyran da gwamnatin ta yiwa kundin zaben kasar dangance da shawarwarin da aka tsayar a taron majalisar CNDP.
Sune wadanda suka tsaya akan bukatar kara yawan wakilan bangarorin siyasa a hukumar zabe da tsarin tafiyar da zaben a karkara. Mataimakin kakakin majalisar Iro Sani ya yaba da cikakken hadin kan da gwamnatin ta samu a lokacin wannan zama.
Rashin cimma dai dai tawa akan wasu mahimman dokokin da gwamatin ta cusa cikin kundin zaben kasar, ya sa ‘yan adawa kauracewa zaman kuri’ar da majalisar ta kira, musamman kan cancantar shiga zabe inji kakakinsu Issouhou Issaka.
Shekaru kusan biyu kenan ake takun saka a tsakanin ‘yan adawa da masu rinjaye, akan maganar sahihancin kundin zabe a Nijar, dalilin da ya sa wasu ‘yan kasar irin su Ibrahim Kantama kiran bangarori akan bukatar su yi karatun ta nutsu.
Kafin shugaban kasa ya saka hannu akan wadanan canji, wajibi ne majalisar dokoki ta gabatar wa kotun tsarin mulki daftarin sabon kundin zaben, domin tantance halarcinsa.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum