Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Tinubu Zai Halarci Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Senegal


Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja ranar Talata zuwa Dakar, Senegal, domin halartar bikin rantsar da sabon zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye.

WASHINGTON, D. C. - A wata sanarwa da mai Magana da yawun shugaban kasar, Cif Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin, ya ce ziyarar shugaban na zuwa ne bisa gayyatar ta jamhuriyar Senegal.

Bassirou Diomaye Faye sabon zababben shugaban kasar Senegal
Bassirou Diomaye Faye sabon zababben shugaban kasar Senegal

Shugaba Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), zai bi sahun sauran shugabannin kasashen yankin domin halartar bikin a cibiyar Diamniadio Exhibition Centre.

Ministan harkokin wajen kasar Yusuf Tuggar da wasu manyan jami'an gwamnati ne zasu raka shi a wannan ziyarar.

Ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya bayan kammala rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin Shugaban kasar Senegal.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG