Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amadou Ba Ya Taya Bassirou Diomaye Faye Murnar Lashe Zaben Senegal


Jagoran 'Yan Adawa A Senegal Bassirou Faye
Jagoran 'Yan Adawa A Senegal Bassirou Faye

Dan takarar gamayyar jam'iyyu masu mulki, Amadou Ba, ya taya abokin hamayyarsa, kuma jagoran 'yan adawa a Senegal Bassirou Faye, murnar lashe zaben shugaban kasar Senegal.

WASHINGTON DC - Wata sanarwa da tawagar masu magana da yawun Ba suka turawa Muryar Amurka ne ya tabattar da hakan, inda ya ce Ba ya kira Faye ta wayar tarho ya yi masa murna.

"Dangane da yadda sakamakon zaben shugaban kasa ya gudana da kuma lokacin da ake jiran sanarwar a hukumance, ina taya Shugaba Bassirou Diomaye Diakhar Faye murnar nasarar da ya samu a zagayen farko na zaben.

"Ina rokon Allah da ya ba shi karfin gwiwa da karfin da ya kamata don ya karbi wannan babban mukami na shugabancin kasarmu.

"Ina yi masa fatan alheri da nasara don jin dadin al'ummar Senegal" a cewar Ba.

A ranar Lahadi 24 ga watan Maris na shekarar 2024 ne aka bude rumfunan zabe a Senegal a zaben shugaban kasa mai cike da rudani, wanda ya biyo bayan rashin tabbas na tsawon watanni da tashe-tashen hankula da suka shammaci kasar dake yammcin Afirka, a matsayin tabbataccen tsarin dimokuradiyya a yankin da ya fuskanci juyin mulki a shekarun baya.

An gudanar da zaben ne makonni bayan da shugaba Macky Sall ya yi kokarin jan lokacin zaben har zuwa karshen shekara, hakar da ta ka sa cimma ruwa.

An hana Sall tsayawa takara karo na uku saboda kayyade wa'adin tsarin mulki.

A saboda haka ne ake kada kuri'a a cikin watan Ramadan, wata mai alfarma da musulmi ke azumi tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG