A ranar Talata kasar Senegal ta wayi gari da sabon zababben shugaban kasa, Bassirou Diomaye Faye, tsohon mai binciken haraji kuma sabon shiga a fagen siyasa wanda ya zaburar da masu kada kuri'a, ciki har da dimbin matasa marasa aikin yi, tare da shan alwashin yaki da cin hanci da rashawa da kuma gyara tattalin arzikin kasar.
Faye mai shekaru 44, ya shiga yakin neman zaben shugaban kasa ne a lokacin da fitaccen dan adawa Ousmane Sonko ya mara masa baya, wanda aka hana shi tsayawa takara saboda wani hukunci da aka yanke masa a baya.
Nasarar zaben shugaban kasar ta ranar Lahadi ta kasance wani gagarumar ci gaba ga Faye, wanda aka saki daga gidan yari kasa da makwanni biyu da suka wuce, kuma yanzu ya zama shugaban mafi karancin shekaru a kasar ta yammacin Afirka.
"Na yi alkawarin yin mulki cikin tawali'u da gaskiya, da kuma yaki da cin hanci da rashawa ta dukkan matakai." Ya fadi haka ne a jawabinsa na farko a daren ranar Litinin a matsayin zababben shugaban kasa, inda ya sake jaddada alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabensa.
"Muna fatan sabon shugaban ba zai sa mu yi taikaci ba," in ji Diakhaté a ranar Talata. "Matasa suna sa fata akan shi sosai."
Duk da cewa ba za a san sakamakon zaben na ranar Lahadi a hukumance ba har sai ranar Juma'a, babban abokin karawarsa tsohon Firayim Minista Amadou Ba wanda ke samun goyon bayan shugaba mai ci Macky Sall - ya amince da shan kaye bisa la'akari da rata mai yawa a sakamakon farko. Ba da Sall duk sun taya Faye murna tare da bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.
Zaben dai ya biyo bayan tashe-tashen hankula da aka shafe watanni ana yi sakamakon kame Sonko da Faye a shekarar da ta gabata, da kuma fargabar cewa shugaban kasar zai sake neman wa'adi na uku a kan karagar mulki duk kuwa da kayyade wa'adin mulkin da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce an kashe mutane da dama a zanga-zangar, yayin da aka daure wasu mutane 1,000.
Sall ya nemi dage zaben har zuwa watan Disamba amma kotun tsarin mulkin kasar ta hana yin hakan, kuma ta tilastawa gwamnati a gudanar da zabe a wannan watan.
Sakonnin Faye na sake fasalin tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa ya gamsar da matasa.
A daren Litinin, Faye ya bayyana wasu muhimman manufofin kasashen waje na farko, wadanda suka hada da yin garambawul ga kungiyar ECOWAS mai fama da rikici a yammacin Afirka.
Sai dai manazarta a Pangea-Risk sun ce rashin samun rinjaye a majalisar dokokin kasar Senegal da kuma wasu sharudan kudi da asusun lamuni na duniya IMF ya gindaya zai hana Faye cike alkawuran da ya yi. Tuni dai Faye ya janye batun samar da kudin kasa, inda ya kara da cewa zai fara neman yin garambawul ga kudin yankin CFA, wanda wasu kasashe 14 na yamma da tsakiyar Afirka ke amfani da su.
Bayan kokarin da Sall ya yi na jinkirta zaben da ya haifar da tsawatarwa daga kotun tsarin mulkin kasar da kuma tashe-tashen hankula a titunan kasar, a ranar 6 ga Maris, gwamnatin kasar ta sanar da cewa za a gudanar da zaben a kafin karshen watan nan. Gwamnatin ta kuma zartar da dokar yin afuwa da ta saki daruruwan fursunonin siyasa da suka hada da Sonko da Faye a ranar 14 ga Maris.
Dandalin Mu Tattauna