Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Rantsar Da Karin Sabbin Ministoci Uku


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da karin ministoci uku da majalisar dattawan kasar ta tantance da su kwanan nan.

Sabbin ministocin uku sun hada da Balarabe Abbas Lawal daga jihar kaduna, Dr. Jamila Ibrahim Bio daga jihar kwara da kuma Ayodele Olawande daga jihar Ondo.

An rantsar da ministocin ne a yayin wani dan kwarya kwaryar biki da ya gudana a fadar shugaban Najeriya ta ASO Rock Villa da ke Abuja.

Balarabe Abbas da aka kai a ma'aikatar muhalli, tsohon sakataren gwamnatin jihar kaduna ne da ya maye gurbin Mallam Nasiru Elrufa'i, wanda tun da farko majalisa ta ki amincewa da shi.

Dr. Jamila wacce matashiya ce yar shekara talatin da bakwai, 'yar siyasa ce da ke fafutukar kawo ci gaba. An tura ta a ma'aikatar matasa, yayin da Ayodele Olawande zai yi aiki a matsayin karamin minista a ma'aikatar matasa.

Jim kadan bayan rantsar da sabbin ministocin ne kuma shugaba Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartaswa a karo na biyu tun bayan rantsar da shi.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG