Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya tabbatar da nadin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya yi hakan ne don sauke nauyin da ya rataya a wuyansa kamar yadda sashe na 3(6) na dokar da ta kafa ICPC a shekara ta 2000 ya tanada, da kuma kara karfafa kokarin gwamnati na yaki da rashawa.
An zabi sabon shugaban hukumar ta ICPC ne don Majalisar dattawan Najeriya ta tantance tare da tabbatar da shi, bayan da shugaban kasa ya amince da bukatar shugaban hukumar mai barin gado na tafiya hutu kafin karshen wa’adinsa daga ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023. A ranar 3 ga watan Fabrairun 2024 ne wa’adin zai kare.
Dakta Musa Adamu Aliyu ya kawo sauye-sauye da yawa a lokacin da yake rike da mukamin babban lauyan gwamnatin jihar Jigawa tun daga watan Satumban 2019.
Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin shugabannin hukumar ta ICPC su kasance masu gaskiya da adalci a gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ko fifita wasu ba.
Dandalin Mu Tattauna