Sai dai masu ruwa da tsaki sun kushe karin kudin kan cewa ya yi kadan.
Bayan wata ganawar sirri ta sa'o'i hudu ne Shugaban Ma'aikatan fadar shugaban kasa kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya ce Gwamnatin tarayya tare da amincewar kungiyoyin kwadago aka ce a kara wa dukan ma'aikatan Gwamnati karin Naira 25,000 kan albashin da suke karba daga wannan wata har zuwa wattani 6 nan gaba.
Gbajabiamila ya ce taron ya amince da wasu batutuwa da ba za a bayyan ba, sai kungiyoyin kwadago sun gabatar da yarjejeniyoyin ga mambobinsu tukuna.
Amma wata Ma'aikaciyar gwamnati a Abuja da ta nemi a sakaya sunanta, ta yi tsokaci kan batun inda ta ce, wannan karin Naira 25,000 idan an hada da mafi karancin albashi na Naira 30,000 duk ba za su saya wa magidanci buhun shikafa ba.
Ta kara da cewa, idan an hada kudin zai zama Naira 55,000 ne kuma abin da kudin zai saya shi ne buhun masara daya.
Ma'aikaciyar ta ce sai an nemi kudin kayan miya da abubuwan da za a sarrafa masaran da shi kafin akai ga ci, saboda haka wannan kudi ba zai taka kara ya karya ba, ko da mata da miji kadai ne a gida.
Shi ma Tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago ta kasa Kwamred Isa Tijjani ya ce wannan duk rudani ne kawai.
A cewarsa, shugban kasa bai bi ka'ida ba saboda babu inda ake irin wannan umurni a gwamnatance kuma a dauka a yi aiki da shi kai tsaye.
Isa ya ce bangarori uku ne ke amincewa da irin wannan umurnin kafin ya zama karbabbe, wato da bangaren gwamnati da na ma'aikata da kuma na masu daukan aiki, saboda haka Shugaban kasa ba shi da hurumin yin irin wadannan bayanai kai-tsaye haka kawai.
Ya kuma ba da shawara ga Shugaba Tinubu da ya bi a hankali saboda a samu a warware matsalolin kasar.
Amma ga kwararre a fanin zamantakewan dan Adam kuma mai nazari a al'amuran yau da kullum Abubakar Aliyu Umar ya yi suka ne da kakkausar murya kan cewa wannan kari na 25,000 ba zai sayi komi ba sai man fetur lita 40.
Abubakar ya ce an ba da kudin ta hanun dama ne an kwace ta hanun hagu.
Shugaban Kungiyar Kwadago Joe Ajaero ya ce kungiyar za ta kai alkawuran da gwamnati ta dauka ga sauran sassanta domin tantancewa kafin ranar uku ga wannan wata da ya kamata su shiga yajin aikin baba ta gani.
Sauari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna