Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Soke Lasisin Wasu Kamfanonin Tsaro Masu Zaman Kan Su



Shugaban majalissar sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijer Janar Abdourahamane Tchinai
Shugaban majalissar sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijer Janar Abdourahamane Tchinai

Ma’aikatar cikin gida ta Jamhuriyar Nijar ta haramta ayyukan wasu kamfanoni masu zaman kan su dake kula da harkokin tsaro a dukkan fadin kasar, bayan da ta ce ta janye lasisin da ke basu izinin gudanar da aiki.

Ma’aikatar ba ta bayyana dalilin daukar wannan mataki ba, inda masana harkokin tsaro da masu fafutuka suka bayyana yadda suke kallon lamarin musamman a lokacin da kasar ke fama da kalubalen tsaro.

Kamfanonin da ofishin ministan cikin gida na Nijar ya haramtawa gudanar da aiki sun hada da SECURI COM, GADNET Securite, MANGA Securite, wadanda suke kula da harakokin tsaro a kasar ta hanyar bada hayar masu gadi ga ofisoshin da suka hada da kamfanonin masu zaman kansu, bankuna da ofisoshin jakadanci da na manyan ma’aikatun kasa da kasa.

Haka kuma irin wadannan kamfanoni sukan kula da tsaro a yayin manyan tarurruka da bukukuwa daban-daban a karkashin tsarin da gwamnatin Nijar ta amince da shi kusan shekaru 30.

Wani dan fafutuka a karkashin inuwar kungiyar Sauvons Le Niger Salissou Amadou wanda ya yi na’am da matakin ya ce, yanayin da ake ciki a yau a kasar ya kai matsayin da tilas gwamnati ta bi irin wadanan kamfanoni sau da kafa.

Sanarwar ta gwamnatin ba ta fayyace mafarin haramta wa wadannan kamfanoni gudanar da aiki ba. Wakilin Muryar Amurka ya tuntubi Sakataren ma’aikatar cikin gida Soumaila Idi Dan Bouzou ta wayar tarho domin neman Karin haske, amma bai same shi ba.

Tuni dai masana sha’anin tsaro irinsu Abdourahamane Alkassoum suka fara hasashe kan abin da ka iya zama silar matakin gwamnatin ta Nijar.

Akwai kamfanonin tsaro masu zaman kansu sama da 200 da aka kafa a ‘yan shekarun nan a Jamhuriyyar Nijar abin da wasu ke danganta da shi da kasancewarsa wata hanyar samun kudaden shiga, kuma ya samar da ayyukan yi ga wani bangare na dimbin ‘yan kasar.

Wasu majiyoyi na hasashen yiwuwar samun hannun jarin wasu kasashen yammaci a wasu daga cikin kamfanonin tsaro masu zaman kansu a Nijar.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Gwamnatin Nijar Ta Soke Laisisin Wasu Kamfanonin Tsaro Masu Zaman Kansu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG