A yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa da matsalar tsada rayuwa da karancin abinci a kasar wanda ake ganin rikici tsakanin kasar Rasha da Ukraine na daga cikin dalilan dake kara tsananta matsalar.
Najeriya dai na daga cikin kasashen nahiyar Afrika dake fuskantar mumunan tasırin yakin dake tsakanin kasar Rasha da Ukraine musamman a fannin samun wadatar abinci ganin yadda manoma ke kokawa a kan tashin farashin takin noma wanda a akasarin lokuta kamfanoni masu sarrafawa na cikin gida ke shigowa da kayan aikinsu daga kasar Ukriane dake fama da rikici.
Farashin Fulawa, da sauran hatsi sun yi tashin da ba’a taba ganin irin su ba a baya kamar yadda Malama Hannatu manomiya ta bayyana inda ta ce, manoma na cikin matsin rayuwa.
Wani ma’aikaci a kamfanin sarrafa taki ya bayyana cewa tsadar taki na da alaka da tashin farashin dala, tsadar man dizal, rashin kyawun tituna, baya ga rikici tsakanin Rasha da Ukraine inda daga kasar ta Ukraine ake shigowa da kayan aikin sarrafa taki masu mahimmancin gaske.
Masani a fannin aikin noma, Ezekiel Bulus Doka, ya bayyana irin matakan da ya kamata gwamnati ta dauka don kawo sauki cikin wannan yanayi kama daga daukewa manoma haraji a kan taki da dai sauransu.
Sai dai idan ana iya tunawa a cikin watan Maris na wannan shekarar ta 2024 ministan aikin noma da samar da wadatar abinci, Sanata Abubakar Kyari ya jagoranci aikin rarraba hatsi da kuma yin alkawarin cewa gwamnati zata yi duk mai yiyuwa wajen samar da wadataccen abinci ga ‘yan kasa.
A saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:
Dandalin Mu Tattauna