Kwato ayyukan ba karamar gwagwarmaya jami'an kwastan Najeriya karkashin shugabancin Abdullahi Dikko Nde suka yi ba. Kamfanonin da a ka kwato ayyukan daga garesu sun hada da Co-Tecna da Societe General Surveilance da Global Scan da Webfontain dukansu na kasashen waje wadanda dubban miliyoyin nera a kowane wata a ke biyansu wurin gudanar da ayyukan da kwastan ke yi da can.
Shugaban Hukumar Kwastan Alhaji Abdullahi Dikko Nde ya bayyana yadda suka samu nasarar kwato ayyukan. Ya yiwa Allah godiya da iyaye da suka dukufa da addu'a har suka kwato ayyukan daga hannaun turawa wadanda kamar wani mulkin mallaka ne suka yi. Ya ce lamarin ya faru ne wajen shekaru talatin da suka gabata inda ba hukumar kwastan ke yin aikin ba sai dai su rubuta abun da suka gani a takarda. To amma yau ayyukan sun koma hannun kwastan. Yanzu zasu iya aikin da kowa ke yi. Ya ce wannan ba karamar nasara ba ce ga Najeriya da hukumar kwastan.
Dangane da moriyar da Najeriya zata ci Alhaji Nde ya ce na daya kamfanonin wajen ana biyansu kudi da kudaden waje kuma bai cancanta a yi hakan ba domin ayyukan kwastan aka basu. Ita hukumar kwastan bata ce ba zata iya yin ayyukan ba.Yanzu kudaden da ake basu zasu dawo Najeriya, wato mariyar farko ke nan. Kowane wata ana biyansu kwatankwacin nera miliyan dubu biyu da 'yan kai. Wannan yanzu an daina. Moriya ta biyu su kamfanonin kasashen waje ne suna iya fadan asirin Njaeriya a hada baki dasu a yi fasakwaurin wasu abubuwa. Amma yau duk wani labari yana hannun kwastan.
Umar Faruk Musa nada karin bayani.