Rahoton da wata kafar yada labarai a kasar Liberiya ta buga, ya ce Shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf ta dan wuce babban mai kalubalantarta Winston Tubman, a yayin da ake cigaba da kidaya kuri’un zaben shugaban kasar da aka yi ran Talata.
Wata cibiyar yada labarai mai zaman kanta a Liberiya da ake kira "Liberian Media Center", ta fada jiya Laraba cewa Shugaba Sirleaf na da kuri’u wajen 135,000 shi kuma Tubman na da wajen 113,000. Sauran ‘yan takarar na can baya.
Rahoton ya ce wannan sakamakon ba a hukumance ya ke ba. An tattara sakamakon ne daga irin sakamako da aka mammanna a rumfunan zabe a fadin wannan kasa ta yammacin Afirka.
Hukumar zaben Liberiya ta ce za ta fara bayyana sakamako a hukumance daga yau Alhamis, to amman wai ba za a sami cikakken sakamako ba sai ran 26 ga wannan wata na Oktoba.
Idan babu wani dan takarar da ya samu fiye da rabin kuri'un da aka jefa, to za a gudanar da zaben fidda gwani ran 8 ga watan Nuwamba.